✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sauya kotun da ke sauraron shari’ar Ganduje a Kano

Gwamnatin Kano ta ce tana shaidu 15 ƙwarara da za ta iya gabatarwa a duk lokacin da aka buƙata.

Babbar Alƙaliyar Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta sauya kotun da ke sauraron ƙarar zargin badaƙalar kuɗi da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane bakwai.

Mai Shari’a Dije, ta mayar da shari’ar zuwa kotu ta 7 da ke Miller Road ƙarƙashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu.

Aminiya ta ruwaito cewa a baya ana gudanar da wannan shari’ar ce a wata babbar kotun Kano mai lamba 4 da ke zaune a sakatariyar Audu Bako, karkashin jagorancin mai shari’a Usman Malam Na’abba.

Jami’in hulɗa da jama’a na Babbar Kotun Jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya ce, “Ofishin Babban Alƙalin Jihar Kano na da hurumin canzawa shari’a wuri a kowane mataki muddin ba a kai matakin yanke hukunci ba.”

Ya ƙara da cewa, sabuwar kotun da aka mayar da shari’ar tana da hurumin sanya ranar ci gaba da sauraron ƙarar.

An gurfanar da Ganduje da matarsa ​​da dansa da wasu mutane biyar a kan tuhume-tuhume takwas da suka haɗa da cin hanci da kuma karkatar da maƙudan kuɗaɗe daga asusun gwamnati.

Gwamnatin Kano a ƙarar da ta shigar da Ganduje da mai dakinsa da ɗansa, ta ce tana da shaidu 15 ƙwarara da za ta iya gabatarwa a duk lokacin da aka buƙata domin tabbatar da abin da take zargi.