Jihar Bauchi ta sauke shugabanin riko na kananan hukumominta gabanin zaben kananan hukumomin da za yi a watan Oktoba.
Gwamna Bala Mohammed ya amince da sauke dukkannin shugabanin rikon ne nan take a ranar Laraba domin ba wa kowa damar tsayawa takara zaben da ke tafe.
“Bayan fitar da jadawalin zaben kama yadda dokar zabe ta tanada, cewa masu son tsayawa takara su sanar da ita cikin kwana 30 kafin ranar zaben ne”, ya sa aka dauki matakin, inji sanarwar Sakatare Gwamnatin Jihar Bauchi Mohammed Sabiu Baba.
Gwamnan ya umarci tsoffin shugabannin da su mika ragamar kananan hukumoin da Shugabannin Gudanarwa na kananan hukumominsu.
Ya kuma yaba musu bisa aikin da suka yi wa al’umma tare da yi musu fatan alheri a nan gaba.