✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sanya wa Filin Jirgin Saman Minna sunan Tinubu

Kafin sauya wa filin jiragen saman suna, ana kiransa ne da filin jiragen saman Abubakar Imam.

Gwamnatin Tarayya ta sauya sunan filin jiragen saman Minna da ke Jihar Neja zuwa filin jiragen sama na Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinar Labarai a Jihar Neja, Hajiya Binta Mamman ce ta bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar Gwamnan Jihar da ke Minna a ranar Lahadi.

Ta bayyana cewa an sauya wa filin jiragen saman na ƙasa da ƙasa suna ne, domin gudunmawa ta fuskar ci-gaba da Tinubun ya bai wa jihar.

Hajiya Binta ta ce a ranar Litinin ne ake sa ran Shugaba Tinubu zai kai wata ziyarar aiki jihar, inda zai ƙaddamar da filin jiragen saman da aka yi wa gyara da kuma wani wurin da aka ware domin ayyukan noma.

Kafin sauya wa filin jiragen saman suna, ana kiransa ne da filin jiragen saman Abubakar Imam, wani marubuci kuma ɗan jarida wanda ya fara ƙirƙiro jaridar harshen Hausa ta farko a Arewacin ƙasar.

A shekarar da ta wuce ne hukumomin da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama suka ce za su sauya wa wasu filayen jiragen sama 15 na gwamnatin tarayya suna, zuwa sunayen wasu fitattun mutane, ciki har da tsoffin shugabannin ƙasar.

Rahotanni sun ce wasu al’ummar ƙasar sun yi suka ga matakin sauya wa filin jiragen suna, inda suka ɗora ayar tambaya kan tasirin yin hakan ta fuskar tattalin arziki.