Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ayyana neman wanda ake zargi da kashe baturen ’yan sanda (DPO) a yankin Odiemudie da ke Karamar Hukumar a Jihar Ribas, Bako Angbashim, ruwa a jallo.
Ana dai zargin Gift David Okpara Okpolowu, wanda aka fi sani da 2-Baba da yaransa, da kisan DPOn, kuma tuni Gwamnan na Ribas ya sanya tukuicin ga duk wanda ya kai ga kama wanda ake zargin.
Gwamnan ya kuma dakatar da wani basarake mai suna Eze Cassidy Ikegbidi har sai abin da hali ya yi, saboda zarginsa da hannu a kisan.
Fubara dai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar dauke da sa hannunsa kuma ya raba wa manema labarai da yammacin Asabar.
Sanarwar ta ce daga yanzu an dakatar da basaraken saboda yadda yake kyale dan dabar yana cin karen shi ba babbaka a yankin.
Gwamnan ya ce, “A matsayinmu na gwamnati mai sanin ya kamata, ba zai yiwu mu nade hannunmu mu kyale bata-gari su rika cin karensu ba babbaka a fadin jiharmu ba.
“Bugu da kari, mun sanya tukuicin Naira miliyan 100 ga duk wanda ya bayar da muhimmin bayanin da zai kai ga kamawa tare da gurfanar da wanda ake zargi da kisan,” in ji Gwamnan na Ribas.