✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon Firaministan Gabon ya naɗa ministoci

Janar Nguema ya kuma sha alwashin sauya kundin tsarin mulkin ƙasar.

Sabon firaministan Gabon, Raymond Ndong Sima ya sanar da naɗin sabuwar majalisar ministocinsa. 

Mambobin jam’iyyun adawa da wasu tsoffin hadiman hamɓararren shugaban ƙasar Ali Bongo da sojoji na daga cikin ministocin sabuwar gwamnatin.

Sabuwar majalisar ministocin ne za ta tafiyar da gwamnati har zuwa lokacin da sojojin za su miƙa mulki ga farar hula.

Ba a dai san tsawon lokacin da sojojin za su ɗauka kafin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokraɗiyya ba, to amma firaministan ya shaida wa BBC cewa yana ganin cikin shekara biyu masu zuwa.

A lokacin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban mulkin sojin ƙasar, Janar Brice Oligui Nguema, ya ce zai kafa kafa gwamnatin da za ta yi aikin mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuradiyya, tare da sakin fursunonin da aka ɗaure saboda siyasa ko addini a ƙasar.

Janar Nguema ya kuma sha alwashin sauya kundin tsarin mulkin ƙasar tare da kafa taftataccen tsarin zaɓe dai riƙa gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar.

A cikin mako ne ya saki hamɓararen shugaban ƙasar Ali Bongo, tare da ba shi damar fita ƙasashen waje domin duba lafiyarsa.

Ya kuma saki wasu daga cikin fursunonin siyasa da hamɓararen shugaban ƙasar Ali Bongo ya ɗaure kwanaki bayan rantsar da shi.

A watan da ya gabata ne Sojoji suka hamɓarar da Bongo jim kaɗan bayan hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.