✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sanar da ranar bude manyan makarantu a Kano

Mun yi feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka tare da rarraba wa makarantu kayayyakin kare kai daga kamuwa da cututtuka.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar cewa za a bude manyan makarantu na gaba da sakandire na jihar a ranar 26 ga watan Oktoban 2020.

Kwamishinan Ilimi mai zurfi ta jihar, Dokta Mariya Bunkure ce ta sanar da hakan da cewa gwamnatin ta kammala tanadin duk wasu ababen kare kai da ake bukata daga kamuwa da cutar Coronavirus domin tsare lafiyar dalibai da malamansu.

A cewarta, akwai kwamiti na musamman da ma’aikatar ta kafa domin bincike da tabbatar an kiyaye dukkan ka’idodi, wanda tuni ya tsunduma wajen gudanar da rangadin gano matakin shirye-shiryen bude makarantun a fadin jihar.

Ta ce dukkanin manyan makarantun sun shirya tsaf tare da bayar da tabbaci a kan jajircewar da Gwamnatin jihar ke yi na ganin an bude makarantun a bisa tafarkin kiyaye matakan kariya daga kamuwa da cutar Coronavirus.

“Mun yi feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka tare da rarraba wa makarantu kayayyakin kare kai daga kamuwa da cututtuka,” in ji ta.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne makarantun firamare da na sakandire a fadin jihar Kano suka bude bayan shafe tsawon watanni bakwai suna hutun barkewar annobar Coronavirus.