Gwamnati a Najeriya ta sanar da ranar Juma’a 2 ga wata da kuma ranar Litinin 5 ga watan Afrilun bana a matsayin ranakun hutu na bikin Good Friday da Easter Monday.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
A jawabin da Daraktan Yada Labarai da Hulda Jama’a na Ma’aikatar Muhammad Manga ya fitar, ya nemi mabiya addinin Kirista su yi amfani da wannan dama wajen yi wa kasar addu’o’in zaman lafiya da hadin kai.
Yayin da yake taya mabiya addinin Kirista murnar wannan rana, Mista Aregbesola yana kuma kira ga al’ummar Najeriya da su hada hannu da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kokarin da take yi na inganta rayuwar al’umma.
Kazalika, sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba a fafutikar da take yi wajen dakile ayyukan ta’addanci a kasar.
“Matsalar tsaro ta shafi kowa saboda haka nake kira ga dukkanin al’ummar kasar da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon bayan samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar,” a cewar Ministan.