✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Sallah Karama

Ministan Harkokin cikin Gida ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 21 da Litinin 24 ga watan Afrilun 2023 a matsayin ranakun hutu domin shagulgulan Sallah Karama ta bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar, Dokta Shuaib Belgore, a madadin gwamnatin.

Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen taya daukacin al’ummar Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya.

Aregbesola ya kuma yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan halayen tausayi, kaunar juna, yafiya, zaman lafiya, sadaukarwa da sani hakkin mamkwabta da Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar.

“Bai kamata kyawawan halaye irin na sadaukarwa da kaskantar da kai da kuma kame kai da suke cike da azumin watan Ramadan su gushe bayan tafiyar watan ba, kamata ya yi a ci gaba da su domin kasancewa cikakkun masu imani na gaskiya,” in ji Ministan.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a shirye yake ya mika mulki ga zababbiyar gwamnati mai jiran gado bayan da aka kammala zabe cikin nasara.

Aregbesola ya ce gwamnati za ta ci gaba da iya bakin kokarinta wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin dukkan ’yan kasa da ma baki da ke zaune a Najeriya.