✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bukukuwan Easter: Gwamnati ta ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu

Gwamnati ta kuma bukaci a yi wa Najeriya addu'a a lokacin

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin, 7 da 10 ga watan Afrilu a matsayin hutu albarkacin bukukuwan Easter da Kiristoci za su yi a fadin Najeriya.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Ya bukaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin wajen kwaikwayon halayen sadaukarwa, kaunar juna, yafiya, soyayya, hakuri da zaman lafiya da Annabi Isah (A.S) ya koyar.

Ministan ya kuma bukace su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’o’i na musamman saboda kalubalen tsaron da take fama da su.

“Tsaro sha’ani ne da ya shafi kowa. Saboda haka, nake kira ga ’yan Najeriya da ma ’yan kasar waje mazauna kasarmu da su ci gaba da nuna halin kishin kasa ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan kasa,” in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati na yin duk kokarinta wajen ganin an mika mulki lami lafiya bayan kammala zaben sabuwar gwamnati.