Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata, 11 da 12 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallar Layya a Najeriya.
Ministan Hrkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya, dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore a ranar Alhamis.
- Jirgin karshe ya tashi ya bar shugaban hukumar alhazan Kano da wasu maniyyata 745 a kasa
- Munanan hare-hare 12 da aka taba kai wa gidajen yari a Najeriya
Ya kuma taya dukkan Musulman Najeriya na gida da na ketare murnar zagayowar lokacin.
Aregbesola ya ce, “Ina kira ga Musulmai da su ci gaba da yada halayen kaunar juna, zaman lafiya, tausayi da sadaukarwa, kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya koyar.
“Ina kuma rokon su da su yi amfani da lokacin wajen yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai da ci gaba, la’akari da halin da ake ciki a yanzu.”
Ministan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta damu matuka kuma tana iya bakin kokarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da kuma inganta rayuwarsu.