Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, ya kaurace wa zaben gwamnan Jihar Osun da ake gudanarwa a Asabar din nan.
Sai dai binciken da wakilan Aminiya suka gudanar ya tabbatar da cewa Aregbesola wanda ke zaman tsohon gwamnan Jihar ta Osun yana kasar Jamus a halin yanzu.
- Duk wanda ya ba mu kudi za mu karba, mu zabi wanda muke so —Mutanen Osun
- KAI-TSAYE: Zaben Gwamnan Jihar Osun
Bayanai sun ce, manema labarai da ke daukar rahoto kan yadda zaben gwamnan ke gudana, sun yi ta zuba idanu don ganin bayyanar Aregbesola a mazabarsa ta Ilesha domin kada kuri’a.
An dai yi zargin cewa, takun sakar da ke tsakanin Aregbesola da magajinsa, gwamna Gboyega Oyetola ne ya sanya ya kauracewa zaben.
Babu shakka an yi ta cece-kucen cewa dangartaka ta yi tsami tsakaninsa da gwamna Oyetola, wanda kuma shi ne ya yi masa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Osun a lokacin da yake gwamna.
Sai dai wata mai taimaka wa Ministan kan harkokin yada labarai, Jane Osuji, ta shaida wa Aminiya cewa ba kaurace wa zaben ya yi ba don a halin yanzu ma ba ya kasar.
A cewarta, ziyarar aiki ce ta kama Ministan da yanzu haka yana kasar Jamus inda yake wakiltar Najeriya a wani taro.