Kotun Sauraron Kararrakin Zabe a Jihar Osun, ta tabbatar da Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yulin bara.
Bayan kammala zaben, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben, lamarin da APC ta ce ba ta yarda da sakamakon zaben ba ta kuma shigar da kara.
- Yarinyar da ta bata a Kaduna an gano ta a Maiduguri
- Sau 66 muna dakile yunkurin yi wa taron Majalisar Zartarwa kutse —Pantami
Yayin da yanke hukunci, Mai Shari’a Tetsea Kume, ya ce INEC ba ta yi amfanin da tanadin da Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zabe suka shimfida ba.
Tuni dai Mai Shari’a Kume ya ba da umarnin sauke Ademola Adeleke, watanni bayan ya sha rantsuwar kama aiki.
Alkali Kume ya umarci INEC da ta karbe takardar shaidar lashe zaben da ta bai wa Adeleke sannan ta mika sabuwar shaidar ga Oyetola wanda ya lashe zabe a halasce.