Kotun Koli ta kori karar da Jam’iyyar PDP ta daukaka na neman soke takarar tsohon Gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola da mataimakinsa Benedict Alabi a zaben ranar 16 ga watan Yuli, 2022.
Wani kwamitin mutum biyar na Kotun Koli, karkashin jagorancin Mai Shari’a Centus Nweze a ranar Alhamis ya bayyana cewa karar da PDP ta shigar ba shi da wani tushe, inda ta umarci lauyan PDP Kehinde Ogunwumiju da ya janye karar.
- CBN ya umarci bankuna su ba da sabbin kudi ta kan kanta
- Harin Masallaci: ‘Dan sanda’ ne ya kashe mutum 101 da bom a Pakistan
Kotun ta ce PDP ba ta da hurumin bin ba’asin hukuncin dawo da takarar Oyetola da Alabi’ a APC a matsayin wanda suka lashe zaben fidd-da gwani.
Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yanke hukunci a ranar 30 ga Satumba, 2022, inda ya soke Oyetola da Alabi a matsayin ’yan takara a zaben gwamna bisa hujjar cewa mukaddashin shugaban Jam’iyyar APC na kasa a wancan lokacin Mai Mala Buni ne ya zabe su don yin takara.
Amma kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin a wani hukunci da ta yanke a watan Disambar bara, hukuncin da PDP ta daukaka zuwa Kotun Koli.
Idan ba a manta ba wata babbar kotun jihar ta soke nasarar Ademola Adeleke a zaben gwamnan jihar, bayan INEC ta rantsar da shi.