An samu girgizar kasa mai karfin maki 4.0 a wasu yankunan Accra, babban birnin kasar Ghana da misalin karfe 11 na dare ranar Laraba 24 ga watan Yuni, 2020.
Mazauna birnin Accra sun kasance cikin fargaba saboda girgizar kasar da tafta akalla sau uku a lokaci guda a yankunan birnin.
Sai dai rohatanni ba su sanar da asarar rai ba ko wata gagarumar asara sakamakon girgisar kasar ba.
Wannan ne karon farko a ’yan shekarun nan aka taba samun irin wannan bala’in girgizar kasa a yankunan birnin Accra kuma duk sun fara lokaci daya.
Wasu masu bibiyan shafukan sada zumunta sun yi ta bayyana fargabarsu game da bala’in.