An tabbatar da sallamar mutumin da aka yi ittifaki shi ne ya fara kamuwa da cutar coronavirus a jihar Kogi daga Asibitin Kasa da ke Abuja bayan ya warke.
Rahotanni sun ce an sallami Sheik Abubakar Ejibunu wanda kuma shi ne babban limamin Kabba da misalin karfe 4:00 na yammacin Asabar.
Wani daga cikin iyalansa ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa tuni mutumin ya sadu da iyalansa ranar Lahadi bayan ya shafe yinin Asabar yana hutawa a Gwagwalada.
- Har yanzu babu coronavirus a Kogi – Yahaya Bello
- A karon farko, an samu bullar coronavirus a Jihar Kogi
Idan za a iya tunawa tun da farko dai an sami ce-ce-kuce tsakanin Hukumar Da ke Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC da kuma gwamnatin jihar kan mutane biyun da suka fara kamuwa da cutar a jihar.
Gwamnatin jihar dai ta sha yin tirjitya kan abin da ta kira kokarin kakaba mata cutar duk kuwa da cewa babu mai dauke da ita a cewar ta.
A makon da ya gabata, gwamnan jihar, Yahaya Bello ya sanar da saka dokar kulle a yankunan da annobar ta bulla a jihar kafin kuma daga bisani ya sanar da janye ta.
Ya ce dokar kullen ta taimaka wa jihar wajen zakulo tare da yin gwaji ga duk wadanda ake zargin suna dauke da cutar wanada sakamakon haka su ka gano babu karin mai dauke da cutar a jihar.