’Yan bindiga sun sako mutum 43 da suka sace daga wani masallacin Juma’a a Jihar Zamfara, bayan sun kashe daya daga cikin mutanen.
A ranar Laraba ’yan ta’adda suka sako mutanen da suka yi awon gaba da su a Babban Masallacin Juma’a na garin Zugu da ke Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.
- Najeriya ta haramta sayar da tikitin jirgin sama da Dala
- An haramta sanya wakar Ado Gwanja a rediyo da talabijin
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, “Daya daga cikin mutane ya rasu a hannun ’yan bindigar bayan sun ajiye su a kan wani tsauni da ke tsakanin yankin Marina da Dajin Barikin Daji da ke Karamar Hukumar Gummi ta jihar.”
Aminiya ta gano cewa da farko ’yan bindigar sun sanya mutanen aikin karfi a gonakinsu, kafin daga basani su amince su sako su bayan tattaunawa tare da biyan Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa.
Wani mazaunin garin ya ce, ’yan bindigar, “Sun sanya mutanen aiki mai wahala ba tare ba su abinci ko hutu ba, mutannen duk a galabaci suka dawo, wasu ko tsayuwa ko ma magana ba sa iyawa.
“Bayan an biya kudin fansa ’yan bindigar suka umarci ’yan uwan mutane su shiga can cikin daji su dauki ’yan uwan nasu a Dajin Barikin Daji.
“Daga nan ne mutanen suka hadu suka tura babura a rukuni-rukuni domin dauko mutanen, saboda suna da yawa.
“Sai da suka bi ta babbar hanyar Daki Takwas zuwa Zuru sannan aka dauko su a motocin da suka ji domin karasowa da su.
“Wani abin takaici shi ne ko rumfar fake wa ruwan sama ba a ba su ba saboda iska ta yi awon gaba da rufin ’yan bokokin da bata-garin suka cunkusa su a ciki.”
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma ya ci a lokacin ba shi da ta ce.