Masu garkuwa da mutane sun sako ’yan uwan marigayiya Nabeeha Al-Kadriyah hudu da suka sace a Abuja bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu.
Da misalin kare 12:30 na daren Asabar ne kannen na Nabeeh suka isa gidansu da ke Abuja, da rakiyar jami’an tsaro.
Kawunsu Sherifdeen, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho da safiyar Lahadi, “An sako ’yan matan ne da yammacin ranar Asabar kuma tuni sun nufi gida”.
Dawowarsu bayan sun shafe kwanaki 19 a hannunsu ’yan bindigar da suka sace su a ranar 2 ga Janairu, 2024 ta sanya murna tskanin al’ummar unguwar.
Sanarwar da Sherifdeen ya sanya wa hannu ta ce, “farin cikinmu game da dawowarsu ba zai misaltu ba, muna godi ga Allah da al’umma da suka ba mu gudunmawa.
“Muna addu’ar samun rahama ga wadanda suka rasu, Allah ya kawo dauki ga iyalan wadanda ke hannun masu garkuwa, ya kubutar da su.”
An yi garkuwa da ’yan matan su biyar ne tare da mahaifinsu, wanda daga bisani masu garkuwar suka sako shi cewa ya kowa kudin fansarsu Naira miliyan 60 cikin kwana uku.
Rashin samun kudaden ya sa suka kashe Najeeba, ’yar aji 500 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, suka kuma kara kudin fansan zuwa miliyan 100, gami da baranar kashe ragowar idan ba a kawo kudin cikin lokacin da suka kayyade ba.
Duk da cewa an biya kudin fansa Naira miliyan 100, masu garku wa da su sun ci gaba da tsare su na tsawon kwanaki, lamarin da ya sanya iyalan cikin zullumi har zuwa daren Asabar.