✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye 106 sun tsere sun bar ’ya’yansu a Gombe — Human Rights 

Galibi an fi samun karuwar iyaye maza da ke guduwa suna barin ’ya’yan da suka haifa.

Alkaluma sun nuna cewa an samu akalla iyaye 106 da suka gudu suka bar ’ya’yansu cikin shekara daya a Jihar Gombe.

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa, National Human Rights Commission (NHRC) ce ta tabbatar da hakan.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gombe, jami’in hulda da alumma na hukumar, Mista Ali Alola-Alfinti, ya ce an samu wannan alkaluma ne a shekarar 2023 da ta gabata.

Alola ya koka kan yadda galibi ake samun karuwar iyaye maza da ke guduwa suna barin ’ya’yan da suka haifa, lamarin da ya ce babban tashin hankali a tsakanin al’umma.

A cewarsa, cikin korafe-korafe 280 da hukumar ta samu a shekarar da ta gabata, bincike ya tabbatar da cewa an samu magidanta 106 da suke tsere suka bar iyalansu.

“Irin wannan lamari yana faruwa da zarar uba ya haifi ’ya’ya ya gaza daukar dawainiyar da ta rataya a wuyansa, sai ya cika bujensa da iska. Kuma wannan lamari yana haifar da matsalar kwakwalwa, inda a zahiri za ka ga mutum kamar lafiyayye amma yana da matsalar kwakwalwa.

“Kuma babbar matsalar da ke haifar da wannan dabi’ar ita ce tabarbarewar tattalin arziki wanda mafi yawan magidanta ke kuka da yanayin matsin rayuwa da ake fuskanta a yanzu.

Sai dai Mista Alola ya yi gargadin cewa, duk wannan hanzari da magidanta ke bayarwa, saba dokar hakkin yara ce uba ya gudu ya bar ’ya’yansa bayan shi ne silar zuwansu duniya.

Ya kara da cewa, ire-iren yaran da iyayensu ke guduwa suna barinsu sukan zama matsala a tsakanin al’umma, lamarin da ya ce akwai bukatar duk masu ruwa da tsaki su tashi tsaye domin yi wa tufkar hanci.

Kazalika, Mista Alola ya bayyana cewa, hukumar ta NHRC za ta dauki matakin hadin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki, a matsayin wani yunkuri na karfafa wa iyaye gwiwa domin ganin sun daure wajen sauke nauyin ’ya’yan da suka haifa.