Wasu ’yan bindiga dauke da makamai a ranar Alhamis sun sace mutum 15 a kauyen ’Yarkatsina da ke gundumar Kekun Waje a Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.
Harin na zuwa ne kusan kwana 36 bayan an kashe sama da mutum 60 a yankin, kuma har yanzu mutanen na tsare a hannun masu garkuwar.
- Uwa ta jefa ’yarta mai shekara 3 a kejin dabbobi a gidan zoo
- ’Yan Najeriya miliyan 19 za su yi fama da yunwa a 2022 —Rahoto
Mazauna yankin sun tabbatar wa Aminiya cewa maharan sun fara zafafa hare-hare ne a yankin bayan ’yan sa-kai sun hana su sakat.
A cewar wani mazaunin yankin mai suna Sadik, “’Yan sa-kan ne suke gadin yankin. Dalilin ke nan da ya sa ’yan bindigar suka ce ba za su saki mutanen ba muddin ba su ajiye makamansu ba.
“Bayan sace mutum 15 din da aka yi yanzu, akwai ’yan kauyen su 76 a ke nan a hannunsu, ciki har da mata da kananan yara.
“Sun tsaya kai da fata sai ’yan sa-kai sun ajiye makamansu muddin suna so su sako mutanen, amma sun shaida musu cewa ba za su ajiye ba, za su ci gaba da kare yankin,” inji Sadik.
Ya ce mutanen kauyen sun dauki darasi ne daga wasu garuruwan makwabtansu da suka ajiye makamansu bayan tattaunawa, amma duk da haka har yanzu ba a fasa kai musu hari ba.
“Wadannan ’yan bindigar ba su da imani ko kadan. Kowace irin yarjejeniya aka yi da su sai sun zo sun kawo hari, shi ya sa muka ki amincewa mu ajiye makaman,” inji shi.
Sai dai duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.