’Yan sanda sun sake gano gawar wani mutum da aka shekara ana cigiyar sa cikin kududdufi a yankin Berom da ke Jihar Filato.
A irin haka ne aka taba gano gawar Manjo-Janar Idris Alkali a Karamar Hukumar Jos ta Kudu ta jihar a shekarar 2018, a wani kududdufi da ake hakar ma’adinai a yankin Dura Dung.
A wannan karon gawar wani mai suna Micheal Danladi ne aka gano a wani kududdufi hakar ma’adinai a Karmar Hukumar Barkin Ladi da ke jihar.
Dan sanda mai gabatar da kara, Mulleng Alex ya yi wa babban shaida ka kisan Micheal Danladi tambayoyi a gaban babbar kotun Jihar a ranar Juma’a.
- Harin Mauludi: Dole a yi adalci ga mutanen Tudun Biri —Sarkin Musulmi
- Kotun Ƙoli: APC da NNPP sun ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya a Kano
Dan sanda mai kula da kes din (IPO) Insp. Jurbe Ezekiel ya bayyana wa kotun yadda ’yan sanda suka shafe kwanaki biyu suna neman gasar a cikin kududdufin kafin su gano gawar Michael Danladi.
Insp. Ezekiel ya shaida wa kotun cewa, “a ranar 25 ga watan Satumba 2022 ne iyalan marigayi Michael Danladi suka sanar cewa ya bace, shi ne ’yan sanda suka fara neman sa.
“Wani abokinsa ya shaida musu cewa Micheal ya amsa wata waya a lokacin da suke tare kafin bacewar tasa.
“Daga nan muka fara bincike inda a muka gano ga lambar da ya yi waya da ita ta karshe ta wani abokinsa ne na kut-da-kut.
“Da muka bincike shi, da farko ya nemi ya musa amma daga baya ya amsa cewa shi ne ya ba da kwangilar a kashe Michael a kan kudi N40,000.
“Ya bayyana cewa shi da kansa ya kai ’yan ina-da-kisan gonar marigayin da ke Maijankai a Barkin Ladi.
“Shi ne kuma ya kai mu kududdufin da muka gano gawar ta rube, muka dauko ta, bayan shafe kwana biyu masu ninkaya suna neman ta a cikin ruwa.”
“Abokin, wanda shi ne babban abin zargi da kuma wanda ya ba wa kwangilar kisan suna tsare a gidan yari a Jos,” in ji shi.
Bayan sauraron shaida na biyu, Mai Shari’a Dawat Shashe’et ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Janairun 2024, domin gurfanar da wadanda ake zargin.