✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Mauludi: Dole a yi adalci ga mutanen Tudun Biri —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya shaida wa Babban Hafsan Tsaron Najeriya cewa za su ci gaba da bibiya har sai an yi adalci ga mutanen da jirgin…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da an yi adalci ga mutanen da harin bom na jirgin soja ya shafa a wurin Mauludi a Jihar Kaduna.

Sarkin Musulmi ya fadi haka ne a Jihar Kaduna a gaban Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, a wurin taron bikin cika shekara 25 na Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad, a kan karaga.

A cikin jawabinsa, Sarkin Musulmi ya ce, ba kawai an hadu ne don yin bikin cika shekara 25 ga Sarkin Jama’a, sai dai don taya shi addu’a tare da yin jajen al’ummar Musulmin da jirgin soji ya kashe a jihar Kaduna.

Sarkin Musulmi ya ce ba a fatan haka ya sake faruwa a Najeriya, inda ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gudanar da kwakkwarar bincike kan dalilin faruwar hakan tare da daukar matakin da ya dace.

“Na yi imanin shugaban kasa zai gudanar da bincike kamar yadda yayi alkawari.

“Don haka muna kira ga jama’a da su jira su ga irin matakin da gwamnatin zata dauka a kai.

“Za mu tabbatar da an yi adalci a kan wannan al’amari, za mu ci gaba da bibiya,” in ji shi.

Ba za mu kara ba —Babban Hafsan Tsaro

Da yake maida jawabi, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya,ce ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen magance sake afkuwar irin haka.

Christopher Musa, ya ce a matsayinsu na hukumar tsaro babban aikinsu shi ne kare rayukan ’yan kasa, don haka wajibinsu ne yin bincike a kan dalilin afkuwar hakan kuma tuni shugaban kasa ya bayar da umurni kan gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.

Allah Ya kare kiyaye wa —Sarkin Zazzau

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Kaduna kuma Sarkin Zazzau, Ambasasa Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce suna nan suna kokari da fafutukar samarwa da sarakuna gurbi a dokar kasa a matsayinsu na wadanda suka fi kusa da al’umma.

Bayan taya Sarkin Jama’a murnar cika shekara 25 kan kujerar sarautar, Sarkin Zazzau ya kuma yi kira kan zaman lafiya tare da yin addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu a harin jirgin saman sojin Najeriya a Tudun Biri ta Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

A cikin jawabinsa, Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad (CON) ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna da irin goyon bayan da take ba su tare da nuna godiyarsa ga wadanda suka halarci taron da sauran wadanda suka bayar da gudummawa kowace iri.

Ya ce babban nasararsa ita ce samun zaman lafiya a yankin tare da samar da abubuwan cigaba da gwamnatoci suka yi a zamaninsa.

Daga cikin mahalarta bikin akwai tsofaffin gwamnonin Kaduna: Kanar Umar Faruk Ahmed da Sanata Ahmed Muhammed Makarfi da sarakunan Kagara daga Jihar Neja da Sarkin Kanam daga Jihar Filato da wakilin Sarkin Keffi daga Jihar Nasarawa.

Sauran sun hada da sarakunan kudanci Kaduna da suka hada da na Chawai da na Kagarko da na Bajju da na Kaninkon da na Barde da na Godogodo da na Gwantu da na Fadan Ayu da na Fadan Kamantan da na Lere da na Saminaka da na Kauru da na Zikpak da na Ninzo da wakilan sarakunan Kagoro da na Morwa (Manchok) da Hakimin Kachia da sarakunan kabilun Ibo da na Yarabawa da ke zaune a masarautar.