Wani wanda ake zargin barawon mutane ne ya sace wata yarinya ’yar shekara 10 ya boye ta a cikin firinji a shagonsa a Jihar Kaduna.
Rundunar ’yan sanda a jihar ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargi da sace yarinyar.
Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, ya ce ranar Asabar, da misalin karfe 2 na rana ne Uwaila Idris mahaifyar yarinyar da aka sace a Unguwar Gara da ke karamar hukumar Kauru ta kawo musu rahoton bacewar diyarta.
ASP Mansir Hassan, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Talata cewa mahaifiyar yarinyar “Ta kai wa ’yan sanda rahoton cewa a ranar 26 ga Afrilu, da misalin karfe 1 na rana wani mai shago da ke unguwarsu ya sace ’yarta mai shekaru 10 mai suna Hanifa a lokacin da ta je shagonsa.
“Amma bayan an gayyace shi ya musanta ganin Hanifa ko sanin inda Hanifa take sannan ya koma shagonsa.
“Bbayan nan ne ya rufe bakinta da Hijabi, sannan ya sanya ta cikin firinji ya kulle ta a ciki da kwado”.
Bayan dawowarsa ne wasu matasan unguwar suka ce ba su yarda ba sai sun bincike shagon.
“Samarin yankin sun dage cewa sai sun bincike shagon, suna cikin binciken ne suka gano Hanifa a kulle a cikin firinji a shagon.
“Zuwa yanzu dai wanda ake zargin yana hannu kuma ana ci gaba da bincike domin gano dalilin aikata wannan mummunan aiki,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Kaduna.
Hassan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu idan an kammala bincike.