Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanar da sake bude wasu kasuwanni bakwai da ta rufe fiye da wata biyu a yunkurinta na ’yaki da ’yan bindigar da suka addabi Jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da kwamishinan yada labarai na Jihar, Ibrahim Dosara, ya fitar a ranar Litinin a Gusau babban birnin Jihar.
Sanarwarwar ta ce an dauki matakin ne duba da saukin da aka samu na matsalolin tsaro da kuma korafe-korafen jama’a kan bude kasuwannin wadanda suke ci mako-mako.
Kasuwannin da aka bude sun hada da kasuwar Nasarawar Burkullu da ta Gusau da Talatan Mafara da Shinkafi.
Saura sun hada da kasuwar Daji da kasuwar Nassarawar Godel da kuma ta Dan Jibga
Sai dai Kwamishinan ya ce bude kasuwannin bai shafi bangaren kasuwar dabbobi ba.
Kazalika, ya ce ba za a lamunci ganin kowa da makami ba kowane iri a cikin kasuwannin.