‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Philip Tataru Shekwo.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Saudiyya na jagorantar taron G20 kan inganta rayuwa bayan COVID-19
- An dakatar da Kwamandan Hisbah kan karkatar da kayan tallafi
- Mahara sun kashe shugaban dalibai a Kaduna
Ya ce, “‘yan bindiga masu yawa da ba a gano daga inda suka fito ba, sun shiga gidan Shugaban APC na Jihar Nassarawa a garin Lafia, ranar Asabar da misalin karfe 11 na dare, suka yi awon gaba da shi, babu wanda ya san inda suka kai shi.”
Mista Bola Longe ya ce an zuba jami’an tsaro a cikin dazukan jihar don ganin an kubutar da Mista Shekwo daga masu garkuwar.
Mazauna yankin Bukan Sidi da ke kwaryar garin Lafiya sun ce maharan sun yi ta harbi a sama don kada su samu kalubale daga jami’an tsaro da ke makwabtaka da wurin.