✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace shanu 390 Na Naira Miliyan 300 A Filato

Sai na baya-bayan nan dai ya faru ne a ranar 31 ga watan Maris, inda aka debe shanu 100 a unguwar Wumatk.

Makiyaya a Karamar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato, sun ce an sace musu shanu sama da 390 na mambobinsu, da darajarsu ta kai sama da Naira Miliyan 300 a wasu kauyukan yankin.

Makiyayan a wannan Talatar sun ce an yi awon gaba da shanunsu a lokacin da aka kaɗa su kiwo a yankunan Bot da Faranti da Anguwan Abuja da Makada da kuma Wumat.

Shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah a Karamar Hukumar Bokkos, Saleh Adamu, ya shaida wa Aminiya cewa, sun kai rahoto ga kwamandan sashin Operation Safe Haven da ke yankin.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Adamu ya ce, “An yi awon gaba da shanun ne a cikin makonni uku.

“A ranar 4 ga watan Maris, an yi awon gaba da shanu 71 a yankin Bot, sai a ranar 11 ga watan Maris, wasu ‘yan bindiga suka saci shanu 93.

“A ranar 17 ga watan Maris kuma an saci wasu shanu 73.

Ya ƙara da cewa, “an sace musu shanu a Anguwan Abuja, a ranar 22 ga watan Maris,

“Sannan kuma an yi awon gaba da shanu kimanin 55. Sai na baya-bayan nan dai ya faru ne a ranar 31 ga watan Maris, inda aka debe shanu 100 a unguwar Wumatk.

Ya tabbatar da cewa an yi wannan ta’asar ne a cikin makwanni uku.

Da yake jawabi kan faruwar lamarin, shugaban kungiyar GAFDAN na Jihar Filato, Garba Abdullahi, ya ce “an kai wa ‘yan kungiyarmu hari.

“Ana sace mana shanu yadda aka ga dama, baya ga shanu 390 da aka sace a Bokkos, mun kuma yi asarar shanu sama da 100.”

Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kawo ɗauki ga al’ummar Fulani a Jihar Filato.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke wanzar da zaman lafiya a jihar, Manjo Samson Zhakom, game da afkuwar lamarin, sai dai haƙar ba ta cimma ruwa ba.