Mahara sun kai farmaki masallaci tare da sace mutum hudu a garin Tella da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba, a daren ranar Laraba.
Wani mazaunin garin Tella, Suleiman Rabiu ya shaida wa Aminiya cewa wasu ’yan bindiga kimanin 12 ne suka zagaye masallacin a lokacin da ake Sallar Isha’i, sannan suka yi garkuwa da mutum hudu.
- Sarauniyar Kyau: An yi wa Hisbah ca kan gayyatar Shatu Garko
- Naira biliyan 305 muke bukata don gudanar da zaben 2023 —INEC
Majiyar ta bayyana cewa bayan katse mutane yayin da suke sallah, maharan sun yi awon gaba da wasu mutane a masallacin.
Mutumin ya ce jim kadan bayan tafiyarsu, ’yan bindigar suka saki mutum daya daga cikin mutum hudun da suka sace.
Mazauna yankin Gassol na fuskantar hare-haren ’yan bindiga da ke zargin wadanda suka yi kaura ne daga Jihar Zamfara bayan fatattaka da suka sha a hannun dakarun sojin kasar nan a baya-bayan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa cikin sati uku an yi garkuwa da sama da mutum 25 wadanda yawancinsu manoma da ’yan kasuwa ne daga yankin.
Mutane da maharan suka yi garkuwa da su yayin sallar Isha’i a a masallacin sun hada da Alhaji Yahaya, Aminu Dali da Alhaji Hussaini, wanda shi ne shugaban masu sayar sa kayan hatsi na yankin.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin.