✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace matar kanen Sanata Babba Kaita

“A jimlace dai, sun kwashe matan aure biyu da yara biyu.”

’Yan bindiga sun kai hari garin Kankiya na jihar Katsina, inda suka sace mutum hudu, ciki har da matar kanen Sanata Ahmed Babba Kaita, dan Majalisar Dattijai mai wakiltar mazabar Katsina ta Arewa.

Sanatan dai shi ne ke wakiltar mazabar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito.

Wani mazaunin garin na Kankiya, Muhammad Sani, ya ce maharan sun shiga garin ne da sanyin safiyar Litinin, sannan suka rika harbi kan mai uwa da wabi.

A cewarsa, an kai harin ne kusa da unguwar Bakin Kasuwa, sannan suka yi wa gidan Mani Babba Kaita kawanya, wanda kane ne ga Sanatan, sannan suka dauke matar shi.

Muhammad ya kuma ce maharan sun shiga gidan wani mai suna Sabe Halilu da ke da matwabtaka da su, inda suka lakada wa matarsa duka suka kuma tafi da ’ya’yansa biyu.

Shi ma wani mazaunin yankin, Salisu Musa, ya ce ’yan bindigar sun kuma sace wata matar aure a unguwar.

Ya ce, “A zahiri gaskiya kanen Sanatan suka je sacewa amma ya samu ya gudu. Daya daga cikin matansa ma ta samu guduwa.

“Amma ita wacce azal din ta fada wa mai suna Farida ta ga cewa idan ta gudu za ta bar ’ya’yanta, dalilin ke nan da ya hana ta guduwa har suka sami kama ta.

“Ita kuwa daya matar, lokacin da suka je gidanta mijinta ba ya nan, sai suka yi mata duka sannan suka kwashe ‘ya’yanta biyu.

“A jimlace dai, sun kwashe matan aure biyu da yara biyu,” inji Salisu Musa.

Garin Kankiya dai na kan hanyar Katsina zuwa Kano.

Kodayake wannan ba shi ne karo na farko da ake kai wa garin hari ba, amma ba kasafai ake kai masa farmakin ba, in aka kwatanta shi da sauran kananan hukumomin jihar.

Sai dai da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah kan lamarin, bai daga wayarsa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.