’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matan aure takwas a wata gona a Karamar Hukumar Kuje da ke Yankin Babban Birnin Tarayya.
An yi awon gaba da matan auren ne kwanaki kadan bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kwali da wasu mutum shida daga kauyen Yewuti.
Wani mazaunin kauyen Gwombe da ke masarautar Gwargwada Usman Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.
Ya ce matan auren suna tsaka da shuka iri ne ’yan ta’adda dauke da bindigogi kirar AK-47 suka yi musu kawanya suka yi awon gaba da su zuwa inda ba a sani ba.
- Abba ya sake gabatar da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin Kano
- Zan dawo da martabar ilimi a Zamfara — Dauda Lawal
Wani basarake daga wani kauye a masarautar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace matan.
“Hakika, hudu daga cikin matan ’yan gida daya ne,” a cewarsa,
Ya ci gaba da cewa, “ina zargin wadannan ’yan bindiga da suka yi garkuwa da matan na daga cikin wadanda suka tsere daga kauyen Kabbi da ke makwabtaka da su da suke yawo a cikin daji bayan ’yan bangar Miyetti Allah suka kashe wasu daga cikinsu a karshen mako.”
Babu wani martani daga kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, kan lamarin.