Ana zargin ’yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya da dama yayin da suka datse babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Juma’a.
Babu wasu cikakkun bayanai game da faruwar lamarin, sai dai rahotanni sun bayyana cewa ya auku ne da misalin karfe 4.00 na yammaci.
Aminiya ta ruwaito cewa, shaidun ganin da ido sun ce ’yan bindigar sun kai wa matafiyan hari ne daura da Kauyen Kare da ke babbar hanyar inda suka yi awon gaba da mutane da ba a iya tantance adadinsu ba.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa, motar da matafiyan da lamarin ya rutsa da su ke ciki an barta yashe a gefen hanya.
Majiyar ta ce, “ba mu da masaniya a kan adadin mutanen da ake sace, amma motar da suke ciki har yanzu tana nan a gefen hanya kuda da Kauyen Kurmin Kare inda lamarin ya faru,” inji ta.
Kazalika, tsohon wakilin shiyyar Kaduna ta Arewa a zauren Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wani sako da ya wallafa ranar Juma’a a shafinsa na Twitter.
“Yanzu aka kira aka sanar da ni cewa ’yan bindiga sun datse hanyar Kaduna zuwa Abuja, tsakanin garin Jere da Kauyen Katari da tsakar rana.
“An yi awon gaba da mutane da dama yayin da wasu matafiyan suka rika juyawa da ababen hawansu cikin hanzari saboda harbin bindiga,” a cewarsa.
Sai dai yayin da aka tuntubi jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammad Jalige, ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a yayin da suke zaman jiran karin bayani daga DPO na ’yan sandan yankin.