✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace mata 20 a wurin taron suna a Katsina

Akalla mata 20 da ke halartar taron suna ne aka yi awon gaba da su.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mata 20 da ke halartar taron suna a kauyen Gidan Bido, a Jihar Katsina.

Mazauna kauyen da ke Karamar Hukumar Dandume sun ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe daya na dare, ranar Juma’a.

“Matar dan uwana, ’yar uwar mai jegon ce, ba ta samu zuwa gidan ba ranar sunan, sai washegari da ta je ta samu labarin abin da ya faru,” inji majiyar tamu.

A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kuma yi garkuwa da maza biyar a sranar Asabar a kauyen Unguwar Bawa da ke Karamar Hukumar ta Dandume.

Wani mazaunin Unguwar Bawa ya shaida wa Aminiya cewa kauyen ne mahaifar Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsin mai wakiltar Dandume.

Sai dai Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce labarin kanzon kurege ne.

“Yanzu na yi magana da DPO din Dandume, kuma ya shaida mini cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru a yankin da ke karkashin kulawarsa.

“Mu kiyayi labarun da ke yawo a kafafen sada zumunta saboda a wasu lokutan ba sa kiyaye ka’idojin aikin jarida,” inji shi.

Ya bukaci masu yada labarai a shafukan sada zumunta da zu rika zuwa wuraren suka gudanar da binciken kwakwaf, ko kuma tuntubar mahukunta domin samun tabbaci a kan labaran da za su wallafa.