Kimanin mutum 13 ne suka fada tarkon wasu ’yan daban daji da suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ce aka yi garkuwa da mutanen wadanda Ma’aikatan Karamar Hukumar ta Zariya ce a kan hayarsu ta zuwa ta’aziya a garin Idasu.
- Matsalar Tsaro: Sabuwar barazana ta kunno kai a Najeriya — Magashi
- Wasu matasa sun guntule wa juna hannu a Yobe
Bayanai sun ce batan hanya ya sanya Ma’aikatan suka nemi wani da ke haye a kan babur da ya yi musu kwatance, ashe abun nema ne ya samu kasancewar mutumin da suka nemi taimakonsa dan koran masu garkuwa da mutanen ne.
Daga bisani masu garkuwar sun sako direban mai suna Umara Abubakar wanda aka fi sani da Katako domin ya kawo rahoton halin da ake ciki kasancewar yankin da abun ya faru na daga cikin wuraren da katse layukan sadarwa ya shafa a Jihar ta Kaduna.
Daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su ciki har da Shugaban Sashen Ilimi da Walwalar Jama’a mai suna Dabora Mugu, da Dalhatu Aliyu Awai Mataimakin Shugaban Sashen Ilimi.
Sai dai yayin da Aminiya ta tuntubi Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim don jin ta bakinshi, ya ce sun shiga dakin taro amma daga baya zai yi waiwayi wakilinmu.
Kawo yanzu da babu wata sanarwar a hukumance da tabbatar da faruwan lamarin domin har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Shugaban Karamar Hukumar bai waiwayi wakilinmu ba.