✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Sace Limami A Jihar Kogi

An sace limamin ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin bayan ya dawo daga Masallaci.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace babban limamin yankin Iyara da ke Karamar Hukumar Jimu a Jihar Kogi, Sheikh Quasim Musa.

’Yan bindigar sun kai farmaki gidan malamin ne a ranar Litinin 25 ga Maris, 2024, inda suka yi awon gaban da shi kuma har yanzu babu amo ballantana labarinsa.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe, jim kadan da isa gidansa da karfe 10 na daren ranar Litinin.

Jami’in hulda da jama’a a kungiyar ci gaban Iyara, Mista E.K. Adebayo ya ce ’yan bindigar sun afka gidan malamin ne kuma suka yi nasarar awon gaba da shi.

“An sace limamin ne da misalin karfe 10 na daren ranar Litinin bayan ya dawo daga Masallaci a kofar gidansa da ke Ilukpa a Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa suna ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da limamin da aka sace.

“Kwamishanan ‘yan sanda a jihar Kogi ya tura tawagar ƙwararru daga sashen ɗaukar matakan gaggawa da mayar da martani tare da ‘yan bangar yankin domin ganin an ceto malamin cikin koshin lafiya,” in ji kakakin.