✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace dalibai a hanyar makaranta a Katsina

An yi garkuwa da mutane 31, ciki har da daliban sakandare da ke hanyarsu ta zuwa makaranta a Karamar Hukumar Bastari ta Jihar Katsina

An yi garkuwa da mutane 31, ciki har da daliban sakandare da ke hanyarsu ta zuwa makaranta a Karamar Hukumar Bastari ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna a safiyar ranar Juma’a ce mahara kusan 40 a kan babura suka far wa kauyen Karare, inda suka kashe mutum daya suka sace wasu 31, ciki har da kananan yara da kuma mata.

Daga cikin yaran da aka yi garkuwa da su har da dalibai daga kauyen Kokiya da ke hanyarsu ta zuwa Makarantar Sakandaren Je-ka-ka-dawo ta Gwamnati da ke kauyen Karare.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, al’ummar kauyukan Kokiya da Karare ba su gama tantance yawan wadanda aka yi garkuwa da su ba.

Shugaban Karamar Hukumar Batsari, Yusuf Yanji, ya tabbatar wa Aminiya da aukuwar harin, amma ya musanta cewa akwai ’yan makaranta a cikin wadanda aka sace.

Mun nemi samun karin bayani daga kakakin ’yan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma ya ce ba shi da labari.

Sai dai ya ce zai tuntubi DPO na yankin ya ji abin da ke faruwa sannan ya waiwayi wakilinmu.

Wasu mazauna garin Katsina da Aminiya ta zanta da su sun bayyana damuwarsu kan yawaitar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, satar shanu da kuma kisan babu gaura, babu dalili a jihar.