Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa kimanin Dala biliyan uku sun yi batan-dabo a kwangilar da kamfanin Mai na NNPC ya gudanar da kamfanin bunkasa sarrafa kayayyaki na NPDC.
Osiinbajo ya ce an sace makuden kudin ne wanda ya kai kimanin kashi 10 na kudin ajiyar kasar a zamanin tsohon shugaban kasar, Goodlyuck Jonathan.
Mataimakin shugaban kasar ya yi furucin ne a taro na bakwai na hadahadar ciniki na kamfanoni masu zaman kansu wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa, jiya.