✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace amarya da ango bayan mako daya da bikinsu a Katsina

An sace amaryar da angonta bayan mako daya da shagalin bikinsu.

A ranar Litinin ne wasu ’yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne suka sace wata amarya da angonta, mako daya bayan bikinsu a Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Rahotanni sun ce amaryar da aka sace mai suna Zainab Isma’il da angonta Sama’ila Abdullahi, ya zuwa yanzu masu garkuwar ba su tuntubi iyalansu ba.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai cewa suna yin iyaka bakin kokarinsu wajen ganin sun bai wa al’ummomi masu rauni kariya daga aukuwar ire-iren wannan ababe na ta’addanci.

Ya ce maharan sun kai farmaki ne kan garuruwa daban-daban lokaci guda a wani shiryeyyen hari wanda ya jefa jami’an tsaron cikin tsaka mai wuya ta dakile dukkan hare-haren baki daya.

Gambo ya nemi mazauna yankunan da su taimaka wa jami’an tsaro wajen tsamo mutanen cikinsu da ke bai wa ’yan bindigar bayanan sirri game da al’ummominsu.

Ya bayar tabbacin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da fadi-tashin ganin sun dakile duk wani hari a fadin Jihar.

Jihar Katsina ta kasance daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da hare-hare ’yan bindiga ya yi kamari.

A cikin ’yan shekarun nan rayukan daruruwan mutane sun salwanta yayin da dama suka fada komar masu garkuwa da neman kudin fansa a yankin.

Hare-haren na ci gaba da aukuwa babu sassauci duk da karin sojoji da sauran jami’an tsaro da ake tura wa yankin.