Mahukunta a Jihar Kano sun sanya dokar takaita tadin samari da ’yan mata da ma zawarawa zuwa kwana biyu a mako a unguwar Tudun Yola da ke Karamar Hukumar Gwale.
Sabuwar dokar, dauke da sa hannun Dagacin Tudun Yola, Malam Nasidi Hamisu, ta ayyana karfe 8 na dare a matsayin lokacin kammala hirar, wadda kuma dole ta kasance a kofar gidansu budurwar ko bazawarar.
- Abin da ya sa ’yan mata ke son auren mazan da suka manyanta
- Yadda ’yan bindiga suka yi garkuwa da masu hakar ma’adinai 100 a Zamfara
- ’Yan bindiga sun sace mutum 55 a kauyukan Katsina
Abubuwan da dokar wadda ta game zawarawa da samari da ’yan mata ta kayyade su ne:
- Takaita yin tadi zuwa ranakun Alhamis da Juma’a kadai
- Lokacin tadi shi ne karfe 5 na Yamma zuwa 8 na dare
- Budurwa ko bazawara ba za ta yi zance a ko’ina ba sai kofar gidansu
- An haramta kidan DJ, idan kuma ya zama dole, sai da izinin Mai Garin Tudun Yola da ’yan banga
- Ta’ammuli da kayan maye ya haramta a unuguwar
- An kuma haramta sayar da kayan maye a daukacin yankin.
Dokar ta hana hira barkatai din wadda ta ce babu sani, ba sabo ga masu karya ta, ta samu goyon bayan jama’ar unguwar da Hukumar ’yan sanda da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Kwayoyi (NDLEA) da ’yan kato da gora da sauransu.
A shekarun baya an sanya irin wannam dokar a unguwar Fagge, inda lokacin aka hana samari da ’yan mata hirar dare.
Muddin saurayi da budurwa na son yin hira to sai dai su yi da safe, rana ko yamma, amma babu hirar dare.
Daga lokacin ’yan kato da gora suka fara aikin hukunta duk saurayi da budurwa da aka samu suna zancen dare ta hanyar yi musu bulala ko kuma a kai su ofis a yanka musu tara