Gwamnatin Faransa ta bayar da umarnin rufe wani masallaci bayan da hukumomin masallacin suka yada bidiyon la’antar malamin da aka kashe ranar Juma’ar makon jiya bayan da ya nuna zanen barkwanci na batanci ga Annabi (SAW).
Masallacin Pantin da ke Arewacin Paris, gwamnati ta ce za a rufe shi na tsawon wata shida daga shekaranjiya Laraba.
- Fim din batanci: A shirye nake na biya a cire ni —Yakubu Muhammed
- An fille kan malamin da ya yi batanci ga Annabi
An yada bidiyon ne kafin a kashe malamin darasin tarihi mai suna Samuel Paty.
Bidiyon ya yi kiran daukar mataki tare da bayyana adireshin makarantar da malamin yake.
Hukumomin masallacin daga baya sun cire bidiyon daga shafin Intanet tare da yin Allah wadai da kashe shi.
Kisan malamin ya haifar da zanga-zanga a sassan Faransa domin nuna goyon baya ga malamin da kuma kare ’yancin fadin albarkacin baki.
An kashe matashin da ya kai harin mai shekara 18, wanda aka bayyana dan gudun hijira ne daga Rasha amma dan asalin kasar Chenchenya.
Rundunar ‘Yan Sandan Yaki da Manyan Laifuka ta Faransa ta ce abin ya faru ne a wata makaranta mai suna Conflans Saint-Honorine da ke Arewacin Paris, babban birnin kasar.
Rundunar ta ce abin ya samo asali ne bayan malamin da aka fille wa kai ya nuna zanen batancin a cikin aji yayin da yake bayar da darasin tarihi.