Yayin da takaddamar sanya hijabi ga dalibai mata ke kara kazancewa a Jihar Kwara, Gwamnatin Jihar ta sanar da sake rufe makarantu 10 da suka nuna tirjiya a jihar har sai abin da hali ya yi.
Tun da farko dai Gwamnatin ta ba da izinin sake bude a makarantun, wadanda galibinsu na kungiyoyin Kiristoci ne ranar Litinin, 8 ga Maris, 2021.
- Farashin gangar danyen mai ya haura $71.28 a kasuwar duniya
- COVID-19: Abubuwa 7 da ya kamata Ku sani a kan rigakakin AstraZeneca
Sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun ki amincewa su bi umarnin, sun kuma sha alwashin kin amincewa da sanya hijabi a makarantunsu na ’yan mata.
Wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi da Ci Gaban Al’umma ta Jihar, Kemi Adeosun ta fitar ranar Litinin, Gwamnatin ta umarci makarantun da su ci gaba da kasancewa a rufe.
“Saboda haka, gwamnati tana umartar dalibai da malaman makarantun da lamarin ya shafa da su zauna a gida har sai lokacin da aka umarce su su dawo.
“Gwamnati ta damu matuka da tabbatar da adalci, daidaito da girmama hakkoki da ’yancin kowane dan kasa,” inji ta.
A ranar 9 ga watan Fabrairun 2021 ne gwamnatin ta fara rufe makarantun saboda takun sakar da ake yi kan sanya hijabin inda ta kafa kwamitin da zai duba lamarin.
Kazalika, a ranar 26 ga Fabrairu, gwamnatin ta sanar da ranar 8 ga watan Maris a matsayin ranar sake bude makarantun, inda ta ce dole su amince da yin amfani da hijabin a matsayin kayan makaranta.
Makarantun da umarnin ya shafa sun hada da:
- Kwalejin C&S da ke Sabo Oke
- Sakandiren St. Anthony da ke kan hanyar Offa
- Makarantar ECWA School da ke Oja Iya
- Makarantar Sakandiren Baptist ta Surulere Baptist
- Makarantar Bishop Smith da ke Agba Dam
- Sakandiren CAC da ke titin Asa Dam
- Makarantar St. Barnabas da ke Sabo Oke
- Makarantar St. John da ke Maraba
- Makarantar St. Williams da ke Taiwo Isale
- Makaranatar St. James da ke Maraba