Majalisar Dokokin Najeriya ta rufe harabarta domin yin feshin magani sakamakon zargin bullar cutar coronavirus.
Sanarwar hakan da hukumar gudanarwar majalisar ta fitar ta hannun wani mataimakin Darekta Titus Jatau ta ce za a rufe harabar Majalisar Wakilai na tsawon kwanaki biyu domin aikin feshin.
“An ba da izinin yin feshin maganin zango na biyu gobe (yau) Alhamis 18 da Juma’a 19 ga watan Yuni, 2020.
“Saboda haka ake bukatar dukkan ma’aikata su bar harabar a tsawon lokacin, su dawo aiki ranar Litinin”, inji sanarwar.
Matakin ya jawo cece-ku-ce game da yiwuwar bullar cutar coronavirus a majalisar, yayinda wasu ke ganin hakan na da alaka da rasuwar Sanata Sikiru Adebayo Osinowo wanda cutar ta yi ajalinsa ‘yan kwanakin nan.
Sikiru Osinowo Dan Majalisar Dattawa ne Mai Wakilar Legas ta Gabas.