Gwamnati ta rufe hanyoyin sadarwar wayar tarho ta GSM a kananan hukumomi 13 a Jihar Katsina.
Hakan ba zai rasa nasaba ba da makamancin matakin da aka dauka a Jihar Zamfara, a yayin da gwamanti ke ta kokarin ganin sojoji sun ragargaza ’yan bindigar da suka addabi yankin Arewa ta Yamma.
- Yawi Modu: An kama dan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo
- ’Yan bindiga sun yaudari jama’a da kiran sallah sun kashe su
An rufe layukan wayar ne a Kananan hukumomi 13, ciki har da guda 10 da matsalar ’yan bindiga ta fi kamari, sai wasu uku da ke iyaka da Jihar Zamfara da kuma Kaduna wadanda kowacce daga cikinsu ke fama da matsalar ’yan bindiga.
Kananan hukumomin 10 su ne: Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da kuma Kurfi.
Dajin Rugu ya ratsa ta kananan hukumomin 10 kuma saboda girman dajin ya zama matattarar ’yan bindiga.
Sauran kananan hukumomin kuma su ne: Funtua, Bakori da kuma Malumfashi.
Matakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta karyata ji-ta-ji-tar da ke yawo cewa ta rufe layin sadarwa a fadin Jihar Katsina.
Da take karyata labarin, NCC ta ce takardar da ta yi ta yawo a kafafen sada zumunta, wadda ta fitar ce a kan rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara amma wasu suka yi wa takardar suddabaru.
A ranar 3 ga watan Satumba NCC ta ba da umarnin rufe layukan sadarwa kacokan a fadin Jihar Zamfara.
NCC ta ce yin hakan ya zama dole domin ba wa hukumomin tsaro damar murkushe ayyukan bata-garin da ke barazana ga sha’anin taro —wato ’yan bindiga.