Da karfe 12.00 na daren Laraba, 15 ga watan Yuli, aka rufe Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust karo na farko.
Maudu’in gasar ta bana shi ne “Matsalolin Mulkin Dimokuradiyya da Dambarwar Siyasa a Najeriya”.
“Dole masu shiga gasar su tunkari wannan batu a cikin labarinsu ta fuskar da suka ga dama, sai dai ana son labarin ya kasance kagagge, ba abin da ya faru a zahiri ba, ko aka fassaro shi daga wani harshe ko wani rubutu na daban”, inji jagoran kwamitin shirya gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi.
Ranar 15 ga watan Mayu ne dai aka bude karbar labarai a gasar, wadda kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya shirya da hadin gwiwar Gandun Kalmomi da Open Arts da ke Kaduna, da nufin bunkasa rubuce-rubucen adabi a cikin harshen Hausa.
Farfesa Malumfashi ya kuma ce zuwa farkon watan Yuli, mutum 218 ne maza da mata suka shigar da labaransu a gasar daga sassa daban-daban na Najeriya da Nijar da kuma kasashen waje, irin su Indiya da China.
“Abin da ya kara fitowa fili shi ne yadda aka tallata gasar, wasu sun turo da labarai cikin Ingilishi da fassara da Hausa, wasu kuma a Ingilishi zalla, musamman ganin tallar gasar cikin Ingilishi”, inji shi.
Daga ranar Alhamis 16 ga watan Yuli ne dai ake sa ran fara tantance labaran da aka shigar.