An rufe Fadar Sarkin Daura, bayan samun rahoton bullar cutar coronavirus a fadar. Daura ce dai mahaifar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke jihar Katsina.
Sakataren gwamnatin jihar Dokta Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan inda ya ce za a sanar da sakamakon wadanda aka yiwa gwajin cutar bayan an bude fadar.
Dokta Mustapha, ya ce “Rufe fadar Sarkin Daura abu ne da aka tsara a duk inda aka samu bullar cutar, sannan bayan rufe fadar an yi wa wasu gwajin cutar” yayin da yin hakan na cikin shirin dakile yaduwar cutar.
- COVID-19: An kafa dokar hana fita a Daura
- Maidakin Sarkin Daura ta rasu
- COVID-19 a Daura: Yadda aka yi musayar zafafan kalamai
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, ya ce an girke jami’an ’yan sanda cikin garin Daura da wasu yankunan jihar don tabbatar da dokar zaman gida da gwamnatin jihar ta sanar.
A ranar 17 ga Afrilu 2020 ne maidakin Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar, Hajiya Binta Umar, ta rasu bayan tayi jinya, ta rasu tana da shekara 70.
A ranar Lahadi gwamnatin jihar Katsina ta sanar da karin mutum takwas wadanda suka kamu da cutar coronavirus, a yanzu haka adadin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta fitar a jihar masu dauke da cutar ya zama 46.