Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa NCDC, ta sanar da rufe dakin gwajin cutar Coronavirus da ke garin Abuja saboda bayyana sakamakon karya.
Daraktan Hukumar na Kasa, Dokta Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana hakan ga Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa mai yaki da cutar, PTF a ranar Litinin.
- An kai mutum 25 gidan yari saboda karya dokar COVID-19 a Kano
- Wanda ya jagoranci sace Daliban Kankara ya mika wuya
- Kwamandan ’yan bindiga Daudawa ya mika wuya a Zamfara
- Sheikh Gumi ya yi wa El-Rufai raddi kan ’yan bindiga
“Idan zaku tuna a 2020 akwai kafar da ta gudanar da bincike kan sakamakon gwajin COVID-19 na karya da ake yi.
“Wannan kalubale ne ga NCDC, PTF da dakunan gwajin cutar.
“A makon da ya gabata ne muka gudanar da bincike tare da gano wani dakin gwajin COVID-19 na bogi, wanda suke karbar kudin mutane suna bayar da sakamakon karya.
“Wadannan dakunan gwajin idan suka dauki gwajin mutane, babu wata hujja dake nuna suna yin gwajin.
“Wannan ba iya damfara ba ce face jefa rayuwar mutane cikin hadari,” a cewar Ihekweazu.
Shugaban na NCDC ya roki ‘yan Najeriya da su kiyayi zuwa dakunan gwajin da hukumar bata amince da su ba, lamarin da ya ce mutane na iya samun cikakken bayanai a shafin intanet na www.covid19.ncdc.gov.ng.
Ya kara da cewa NCDC za ta ci gaba da goyon bayan jihohi da gwamnatin tarayya a fafutikar da suke yi na dakile yaduwar cutar a kasar.