✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe Coci saboda sayar da ‘maganin bindiga’ a Kogi

An ga wasu mutane da dama cikin mari da sunan ana yi musu magani.

Gwamnan Jihar Kogi, Gwamna Yahaya Bello, ya ba da umarnin rufe Majami’ar New Jerusalem Deliverance da ke Okene bisa zargin yaudarar masu ibada tana sayar musu da wani ruwa a matsayin maganin bindiga.

Haka nan, ana zargin majami’ar da bude wani asibitin da gwamnati ba ta san da zamansa ba.

Bayanani sun ce tun a 2008 limamin majami’ar, Peter Adeiza, ya bude asibitin nasa inda ake zargin mutane da dama sun mutu a cikinsa sakamakon rashin kwarewa da rashin tsabta.

A ranar Litinin da ta gabata ne Mai Bai wa Gwamna Shawara Kan Harkar Tsaro, Kwamanda Jerry Omodara (mai murabus), ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa rufe asibitin da kuma majami’ar.

An gano cewa, baya ga karbar haihuwa da masara lafiya, ana kuma amfani da majami’ar wajen karba da yi wa masu lalurar tabin hankali magani.

Sakamakon dirar mikiyar da jami’an suka yi wa cocin, an ga wasu mutane da dama cikin mari da sunan yi musu magani.

Masu ibada a cocin sun yi ikirarin suna samun maganin rashin lafiya mabambanta a wajen limamin cocin nasu.

A cewar Omodara, akwai hujjoji da yawa da suka nuna ayyukan da ke gudana a cocin sun saba wa adddini da tsarin kiwon lafiya.

Ya kara da cewa nan da dadewa ba za a gurfanar da Peter Adeiza a kotu don ya fuskanci hukunci muddin aka kama shi da laifi.