An zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu ’yan kungiyar ISIS a kasar Iraqi.
Hukumomin lafiya a Iraqi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum shida ne aka rataye a ranar Litinin kuma uku daga cikinsu an kama su ne da laifin ta’addanci.
Majiyoyin sun ce an rataye mutanen ne a Gidan Yarin Nasiriyah, inda ake tsare da su a matsayin fursunonin kafin a zartar musu da hukuncin.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce a shekarar da ta gabata, an zartar da hukuncin kisa a kan mutum 45 a kasar ta Iraqi.
Amnesty ta ce akasarin wadanda aka kashe din a bara an zartar musu da hukuncin ne a kan laifin zama ’yan kungiyar ISIS.