✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da Sanata Hassan Nasiha mataimakin gwamnan Zamfara

An zargi tsohon Mataimakin Gwamnan da almundahana da kudin gwamnatin jihar.

An rantsar da Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara.

Alkaliyar Alkalai ta Zamfara Kulu Aliyu ce ta rantsar da sanatan a rana Laraba bayan ’yan Majalisar Dokokin jihar sun amince da wasikar zabensa da Gwamna Muhammad Bello Matawalle.

Lokacin da ya bayyana a gaban majalisar, an nemi ya rankwafa kuma ya wuce kamar yadda yake a tsari na Majalisu a kasar.

Duk wannan dai na zuwa ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci da majalisar ta yi, jim kadan bayan tsige tsohon Mataimakin Gwamnan, Mahdi Aliyu Gusau.

A zaman na ranar Laraba wanda Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasiru Mu’azu Magarya ya jagoranta, ya karanta wasikar da Gwamna Matawalle ya aike wa majalisar mai dauke da sunan Sanata Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa sabon Mataimakin Gwamnan shi ne wakiltar shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa.

A ranar Laraba ce Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kada kuri’ar tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau.

‘Yan majalisa 20 daga cikin 24 ne suka kada kuri’ar goyon bayan tsige Mataimakin Gwamnan, bayan kwamitin da majalisar ta kafa da ke bincike a kan zargin shi da almundahana da kudin gwamnatin jihar ya gabatar da rahotonsa.

Honarabun Magarya ne ya karanta rahoton da kwamitin ya gabatar a ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa lallai Mataimakin Gwamnan ya yi sama da fadi da kudin gwamnatin jihar.

Ko a Talatar da ta gabata Mataimakin Gwamnan ya ki halartar zaman kwamitin mai mambobi bakwai da ke gudanar da ke bincike a kansa.