Kasar Masar ta nada mata 98 a matsayin alkalai a daya daga cikin manyan hukumomin shari’ar kasar, wato Majalisar Kula da Harkokin Shari’a.
An nada alkalan ne a gaban Alkalin Alkalan Majalisar, Mohammed Hossam el-Din, a wani taro a birnin Alkahira na kasar, a ranar Talata.
- Ruwan wuta ya yi ajalin ’yan bindiga 50 a Birnin Gwari
- Bam ya kashe mutum 13, ya raunata wasu a Siriya
Wanann na zuwa ne bayan Shugaba Abdul-Fattah Al-Sisi, ya yi kira ga mata su shiga manyan hukumomin shari’ar kasar.
Tuni mutane da dama ciki har da masu rajin kare hakkin mata suka fara jinjinawa El-Sissi, kan kiran da ya yi na mata su shiga harkar shari’ar kasar.
Tun bayan kafa majalisar a 1946 dai, maza ne kawai ake nadawa kuma ba a amincewa da mata masu son aiki da majalisar.
Hakan ya sa mata da dama daga ciki da wajen kasar suka dinga sukar tsarin a shekarun baya.