Bayan samun nasara a kan tsohon Shugaban Kasar Jacob Zuma, inda ya sanar da cewa ya yi murabus daga mulki. Majalisar kasar ta nada Cyril Ramaphosa ya zama mukaddashin shugaba.
Shi dai Cyril shi ne shugaban jam’iyyar tun bayan da ya maye gurbin Jacob Zuma a watan Disamba, wanda tun wannan lokacin ake tunanin shi ne zai kuma maye gurbin Jacob Zuma a matsayin Shugaban Kasa idan haqarsu ta kai ma ruwa.