✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sabon Sarkin Musawan Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya amince da nadin Sagir Abdullahi Inde a matsayin sabon Sarkin Musawan Katsina. Hakan na kunshe cikin…

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya amince da nadin Sagir Abdullahi Inde a matsayin sabon Sarkin Musawan Katsina.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sallaman Katsina, wanda kuma ya kasance Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello Ifo.

Sanarwar ta ce, “Muna sanar da al’umma daga yau Talata 22 ga watan Satumban 2020, Sagir Abdullahi Inde ya zama Sarkin Musawan Katsina.

“Allah Ya taya shi riko Ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyansa”.

Sabon nadin ya biyo bayan mutuwar tsohon Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman, a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020.