Al’ummar Hausawan garin Ile-Ife a jihar Osun, sun yi sabon Sarki mai suna Alhaji Lawan Ishaq Yaro, bayan da Babban Basaraken yankin Onni na Ife, Oba Adeyeye Onitan Ogunwusi ya tabbatar masa da sarautar da safiyar yau Talata a fadarsa da ke garin Ile-Ife.
Nadin sabon Sarkin Hausawan, ya biyo bayan rasuwar tsohon Sarkin Alhaji Mamuda Lawal Madagali, wanda ya rasu a kwanakin baya da fari dai an so a sami hatsaniya da rarrabuwar kai bisa nadin sarautar Sarkin Hausawan na Ile-Ife.
Inda mutum uku suka fito suka nuna sha’awarsu lamarin da yaso ya kawo hatsaniya da tarnaki inda aka gudanar da zanga-zangar lumana a karshen makon jiya sai dai binciken da Aminiya tayi zuwa yanzu hankalin jama’a ya kwanta bayan da babban basaraken yankin Oni na Ife ya jagoranci gabatar da nadin inda ya yi zama da dukkanin bangarorin da suka nuna sha’awar su.